Tinubu ya yi wa ma’aikata ƙarin albashi na wucin-gadi

Tinubu, gwamnati, tarayya, 'yan sanda, jihohi
Gwamnatin tarayya dana jihohin Najeriya 36 na nazari akan bukatar kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi. Hakan ya biyo bayan wani taron gaggawa daya gudana yau...

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa ya amince da karin albashin na naira 25,000 ga ƙananan ma’aikatan gwamnatin tarayya na tsawon wata shida.

Tinubu ya sanar da haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar kasar na ranar murnar cikar kasar shekara 63 da samun yancin kai.

Tinubu wanda a cikin jawabin nasa ya ce yana sane da halin tsanani da al’umma suka faɗa sanadiyyar matakan da gwamnatinsa ke ɗauka, ya ce wajibi ne ‘yan Najeriya su jure hali na tsanani matukar suna son ganin ƙasar ta samu ci gaba.

Wannan ƙarin albashi na wucin-gadi na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ƙwadago a ƙasar suka sanar da aniyarsu ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a cikin wannan mako.

Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon sun zargi gwamnati da rashin cika alkawarin da ta yi cewa za ta ɗauki matakan rage tsananin rayuwa ga al’umma bayan cire tallafin man fetur.

A jawabinsa na kama mulki ne shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, al’amarin da ya sa farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabi, wanda ya haifar da gagarumin tashin farashin sufuri da na kayan masarufi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here