Tinubu ya yi alƙawarin hukunta makisan sojoji a kudancin Najeriya

Tinubu, Shugaban, Najeriya, sojoji, kudancin, hukunta, alkawari
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Manyan jami’an soji 4 da sojoji 12 aka kashe a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya bayan rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu ya sauke Sha’aban daga mukaminsa

“Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar sun samu amincewa ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a mummunan aika-aikar da aka yi kan al’ummar Najeriya” in ji Shugaba Tinubu.

Tinubu ya yi magana ne sa’o’i bayan da kafafen yaɗa labarai suka rawaito cewa wasu ɓata-gari sun cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna wurin suka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.

Karin labari: Mai POS ya maido da Naira Miliyan 10 da akayi kuskuren tura masa

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya shaidawa manema labarai cewa ba shi da masaniya game da harin na ɓata-gari kan yankin na Okuama. Sai dai ya jaddada cewa dole ne sojoji su ƙwato makaman da aka sace daga sojojin da aka kashe.

Wasu yankuna da ba sa ga maciji da juna game da mallakar fili sun sha tafka hatsaniya a makonnin baya-bayan nan lamarin da ya janyo mutuwar mutane kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka sanar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here