Tinubu ya yaba wa majalisa bisa tabbatar da dokar ta-ɓaci a Rivers

0fa57dc7 cc6e 42e0 9283 e5b17a3f88da.jpg

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yaba wa majalisar dokoki bisa tabbatar da ayyana dokar ta-ɓacin da ya yi a jihar Rivers, inda ya ce ƴan majalisar sun yi ƙoƙari wajen ajiye bambancin siyasa tare da fitita matsalar tsaro.

A wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce sun ɗauki matakin ne domin wanzar da zaman lafiya da magance rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar na kusan wata 15.

“Rikicin jihar Rivers ya yi riga ya yi ƙamari, har yake barazana ga kadadorin man fetur, kuma yake yunƙurin kawo tsaiko ga tattalin arziki da mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin da muke yi wajen daidaita ƙasar.

Labari mai alaƙa: Majalisar Dattawa ta amince da dokar ta-bacin da Tinubu ya sanya a Rivers

“Matakin da kuka ɗauka a yau ya nuna cewa ƙasarmu za ta samu nasarori da ci gaba idan aka samu haɗin kai.”

Shugaba Tinubu ya ce dokar ta-ɓacin ta wata shida za ta ba shugaban riƙon damar saita al’amura ne a Rivers, tare da tabbatar da sulhu a tsakanin ɓangarorin da suke saɓani.

Karanta: Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers

Tinubu ya kuma yi godiya ga ƴa Najeriya bisa fahimtarsa da suka yi, sannan ya yi kira da dukkan masu ruwa da tsaki da su goya masa baya wajen mayar da zaman lafiya a jihar ta Rivers.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here