Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya soke shirin yin jawabin ranar Dimukuraɗiyya na bana da zai gudanar a kafafen yaɗa labarai ranar Alhamis din makon nan.
Tun farko an shirya yaɗa jawabin nasa ne kai tsaye domin tunawa da zagayowar ranar dimokuradiyyar Najeriya shekaru 26.
A maimakon haka, zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasa.
An bayyana canjin ne a wata sanarwa da Daraktan yada Labarai da hulda da Jama’a na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Segun Imohiosen ya fitar a daren ranar Laraba.
“Saboda mai girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya shirya halartan taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa, an soke yaɗa jawabin Shugaban kasa a ranar 12 ga Yuni,” in ji sanarwar.
Duk da haka, sauran ayyukan ranar Dimokradiyya za su ci gaba kamar yadda aka sanar a baya.
Sauran abubuwan da za a gudanar ɗin sun hada da lacca da aka shirya gudanarwa da misalin karfe 4:00 na yamma a dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja.













































