A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) guda biyu da mambobin hukumar da’ar ma’aikata ta kasa (CCB) biyu bayan majalisar dattawa ta amince da su.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa shugaban kasar ne ya rantsar da sabbin wadanda aka nada a yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya.
Kwamishinonin INEC guda biyu da aka rantsar sune: Malam Tukur Yusuf mai wakiltar Arewa maso Yamma da Farfesa Sunday Aja mai wakiltar Ebonyi.
Karin karatu: Zargin ɓatanci a shafin sada zumunta: Kotu za ta saurari tuhumar raina umarnin kotu da Sanata Akpoti-Udughan ta yi
An kuma kaddamar da Ikpeme Ndem, daga Cross River da Mai Shari’a Buba Nyaure mai ritaya, daga Taraba a matsayin mambobin hukumar CCB.













































