Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Birgediya Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC).
Bri. Janar Nafiu, har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne babban hafsan hafsoshin sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda kuma ya yi aiki iri daya tare da marigayi babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Raised Abiodun Lagbaja.
Kafin a nada shi shugaban ma’aikata na COAS, ya kasance babban darakta a Kwalejin Soja ta kasa.
Karanta: Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NYSC da wasu mutane a Katsina
Sabon shugaban NYSC ya fito ne daga Ileogbo, karamar hukumar Aiyedire ta jihar Osun.
Nafi’u wanda nadin sa ya fara aiki nan take, ya maye gurbin Birgediya Janar Yushau Ahmed.












































