Tinubu ya naɗa sababbin manyan sakatarori biyar

Tinubu Tinubu sign 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori guda biyar domin cike gibin da ke cikin ma’aikatar gwamnati ta tarayya.

A cewar shugabar ma’aikatan gwamnati ta tarayya, Misis Didi Walson-Jack, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktar sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Misis Eno Olotu, ta fitar a Abuja a ranar Litinin.

Sababbin manyan sakatarori sun haɗa da Ibrahim Ozi daga birnin tarayya Abuja, Ezemama Chidiebere daga jihar Imo, Garba Usman daga yankin arewa ta tsakiya, Mohammed Ishiyaku daga yankin arewa maso gabas, da kuma Ukaire Chigbowu daga yankin kudu maso gabas.

Walson-Jack ta ce an gudanar da tsarin tantancewa da zaɓen waɗannan mutanen cikin gaskiya da bin ƙa’ida, bisa manufar gwamnatin Tinubu ta tabbatar da cancanta da nagarta a cikin ma’aikatar gwamnati.

Ta shawarci sababbin manyan sakatarorin su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta ayyukan gwamnati da kuma tallafa wa shirin ci gaban ƙasa na gwamnatin shugaba Tinubu.

Haka kuma ta yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da gaskiya, cancanta da ƙwarewa a cikin ma’aikatar gwamnati, tana mai cewa wannan naɗin ya nuna aniyarsa ta samar da ma’aikatar gwamnati mai ƙoƙari da bin ƙa’ida domin biyan buƙatun ‘yan Najeriya.

NAN.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here