Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa bisa rasuwar ƴan wasan Kano

Bola Ahmed Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya bayyana kaɗuwarsa bisa hatsari da ya rutsa da tawagar ƴan wasan jihar Kano da ke dawowa daga bikin wasannin kasa da aka kammala a Ogun.

A madadin gwamnatin tarayya, shugaban ya mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Kano, da kuma ga iyalan wadanda suka mutu a hatsarin, ta, cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Mista Bayo Onanuga, ya fitar.

Tinubu ya jinjina wa wadanda hatsarin ya rutsa da su, bisa sadaukarwa da burinsu a wajen bunƙasa harkokin wasanni da jajircewa wajen ciyar da Najeriya gaba.

Ya tabbatar da cewa babbar karramawar da kasa za ta ba su ita ce daukar kwararan matakai don dakile faruwar irin wannan iftila’i a nan gaba da kuma inganta matakan tsaro fannin sufuri.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ba iyalan wadanda suka rasu haƙurin jure rashin, tare da fatan warkewar wadanda suka samu rauni.

A wani labarin makamancin haka, shugaba Tinubu ya bayyana damuwarsa kan ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja, lamarin da ya janyo asarar rayuka tare da raba iyalai da dama da muhallansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here