Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana alhininsa game da rasuwar babban malamin addinin musuluncin nan mazaunin Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Tanshi, yana da shekaru 68 a safiyar yau Juma’a.
Tinubu ya ce malamin ya bayar da gudunmawa wajen gyare-gyaren miliyoyin matasa da sauran musulmi masu imani a kan tsarin addinin Musulunci.
Bayo Onanuga, mai magana da yawunsa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Shugaban ya yaba da kokarin malamin wajen dakile yaduwar munanan ayyukan ta’addanci, musamman a farkon rikicin Boko Haram.
Ya ce musulmi mai imani zai yi matukar kewar muryar sa, yana mai kira da a daidaita dabi’u da halayya.
Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan Tanshi, Tinubu ya bukaci iyalansa da mabiyansa da su yi koyi a cikin kyakkyawan aikinsa. (NAN)