Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Rome, babban birnin ƙasar Italiya, domin halartar babban taron shugabannin ƙasashe na shirin “Aqaba Process”, wanda ke mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci.
Shirin Aqaba Process an ƙaddamar da shi ne a shekara ta 2015 ƙarƙashin jagorancin Sarki Abdullah na biyu na ƙasar Jordan, tare da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasar Italiya.
Babban manufar shirin ita ce ƙara tsaurara matakan tsaro da haɗin kai a yankuna musamman a ƙasashen yammacin Afirka.
Labari mai alaƙa: Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Rome
Taron, wanda za a fara a ranar 14 ga watan Oktoba, zai tattaro shugabannin ƙasashe, jami’an leken asiri da na tsaro daga ƙasashen Afirka, da kuma wakilan ƙungiyoyin gwamnati da na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin tattauna ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da tasowa a yammacin Afirka.
Shugabannin za su tattauna kan yadda za a fuskanci barazanar ta’addanci a ƙasa da kuma a teku, musamman ta fuskar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin da ƙasashen duniya.
Haka kuma, za su tsara dabarun yaki da yada akidar tsattsauran ra’ayi ta hanyar internet da kuma rushe hanyoyin sadarwar Internet da ke tallata ayyukan ta’addanci.
Baya ga halartar zaman taron Aqaba Process, shugaban ƙasa Tinubu zai gudanar da tattaunawa ta musamman da wasu shugabanni domin ƙarfafa haɗin kai wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin yammacin Afirka.
Tare da shugaban ƙasa a wannan tafiya akwai karamar ministar harkokin ƙasashen waje, Bianca Ojukwu, ministan tsaro, Mohammed Badaru, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu; da babban darakta na hukumar leken asiri ta ƙasa (NIA), Mohammed Mohammed, da wasu jami’an gwamnati.













































