Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Tinubu, gana, 'yan kasuwa, najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa da manyan ‘yan kasuwa masu zaman kansu da wasu gwamnonin jihohin ƙasar, inda suka tattauna halin da...

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da gwamnonin ƙasar a zauren majalisar dokoki da ke Abuja.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na safe, ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun.

Karanta wannan: ‘Yan gudun hijirar Sudan na cikin matsanancin hali a Chadi – NRC

Taron dai bai rasa nasaba da damuwar da ake nunawa a fadin kasar dangane da tsadar kayan abinci da rashin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Taron dai ya biyo bayan taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa NEC na wata-wata, wanda mataimakin shugaban kasa Shettima ya jagoranta.

Bayan koke-koke da al’ummar kasar suka yi kan tabarbarewar tsaro da tattalin arziki, shugaban kasar ya umarci ma’aikatar noma da samar da abinci ta saki kimanin tan dubu arba’in da biyu na masara da gero da sauran kayayyakin masarufi a cikin tsare-tsare don magance hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

Karanta wannan: Faransa ta gargaɗi ‘yan kasarta kan tafiya arewacin Mozambique

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da zuba ido kan ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta yi ciki har da cire tallafin man fetur ya zama dole, inda ta kara da cewa wadannan matakan za su haifar da riba nan ba da jimawa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here