“Tinubu ya ce a faɗawa gwamnatin Kano ni ne shugaban APC” – Ganduje

Ganduje, Tinubu, APC, Kano, Gwamnati
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa wanda mazaɓarsa ta ce ta dakatar da shi, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa...

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa wanda mazaɓarsa ta ce ta dakatar da shi, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa ba, yana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ne ya tabbatar masa cewa “kujerarsa na nan daram-dam.

Ganduje ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna shi yana jawabi ga dandazon magoya bayansa da suka kai masa ziyara a gidansa na Abuja domin nuna goyon baya.

Karin labari: Yadda Shari’ar Ganduje Da Gwamnatin Kano Ta Kasan Ce A Yau

Ya ce “jiya na ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu kuma na yi masa bayanin komai kuma ya gode muku abin da kuka yi” in ji Ganduje yayin da yake magana ga magoya bayansa.

“Sannan shugaban ya ce ku yi hakuri, wannan kujerar da suke hari, kujerar tana nan ta zauna daram-dam” in ji Ganduje.

Tsohon gwamnan ya kuma ce Tinubu ya tabbatar masa da cewa kujerar shugabancin jam’iyyar APC ta Najeriya tasa ce kamar yadda ya faɗa “kujerar shugabancin APC ta Najeriya tana kan Abdullahi Umar Ganduje.”

Karin labari: EFCC ta kai samame gidan tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

An nuna magoya bayansa a cikin bidiyon suna ta murna da shewa da tafi yayin da tsohon gwamnan ke gabatar da kalamansa.

A yau Laraba ne dai wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan wasu shugabannin APC tara a mazaɓar ta Ganduje suka shigar da ƙara kan a dakatar da shi bayan wata takardar koke da wani ɗan jam’iyyar Ja’afaru Adamu ya shigar.

Karin labari: KEDCO ta saka hannun jari na Naira Biliyan 1.2 don fadada sadarwa

A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya buƙaci jagororin mazaɓar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da ƙimar jam’iyyar da kuma tasirin da batun zai yi a fafutukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yaƙi da rashawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here