Tinubu ya baiwa shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas muƙami da Felix Morka, da sauran shugabanni

tinubu 2 (2)

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Felix Morka, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Kasa a matsayin Shugaban Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA).

Shugaban ya kuma nada Alhaji Abdullahi Abbas, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano a matsayin shugaban hukumar kula da aikin Gona ta Najeriya.”

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, ba ya ce shugaba Tinubu ya amince da nadin Hon. Fatuhu Mohammed Buhari daga jihar Katsina a matsayin Darakta-Janar na Majalisar inganta noma ta kasa.

Shugaban ya kuma nada wasu jiga-jigan jam’iyyar a matsayin shugabannin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya daban-daban su kimanin 21.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here