Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara kuma jimi’in sake fasalin harkokin kiwo na shugaban kasa.
An sanar da nadin Jega a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga Tinubu kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga da ya wallafa a shafin X a daren Juma’a.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Jega ya kasance shugaban INEC tsakanin 2010 zuwa 2015.
Onanuga ya rubuta cewa, “Shugaba Bola Tinubu ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai bashi shawara kuma jimi’in sake fasalin kiwon dabbobi.”
Idan za a iya tunawa a watan Yulin 2024, Tinubu ya kirkiro wata sabuwar ma’aikatar mai suna Ma’aikatar Raya Dabbobi, inda aikin ma’aikatar zai mayar da hankali wajen samar da hanyoyin magance matsalar manoma da makiyaya da suka dauki tsawon shekaru ana yi.
Wannan ya biyo bayan shawarar da kwamitin sake fasalin kiwo na kasa a Ma’aikatar Albarkatun Dabbobi ya bayar na, a tsakanin sauran abubuwan da za a iya samarwa, ciki har da rage rikicin da ya dauki tsawon shekaru ana yi tsakanin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.