Tinubu ya amince da bada tallafin wankin Ƙoda a asibitoci 11, tare da rage kudin wankin daga Naira dubu 50 zuwa Naira 12 a kowanne zagaye

Dialysis machine 750x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafi kan aikin wankin koda ga ‘yan Najeriya a asibitoci 11, inda ya rage kudin da ‘yan Nijeriya ke kashewa wajen yin wankin daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000.

Wannan tallafi za a aiwatar da shi a duk shiyyoyi na yankuna shida na cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya.

Cibiyoyin da za su amfana sun hada da cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya FMC da ke Ebute-Metta a Legas da cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya FMC da ke Jabi, Abuja da Asibitin ami’ar (UCH) a Ibadan da cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya FMC da ke Owerri, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) da ke Maidugurin.

Karin karatu: Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 28,000 aiki saboda janye tallafin USAID

Sauran sun hada da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya FMC da ke Abeokutada Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LUTH) da Legas da cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya FMC da ke Azare sai Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) da ke Benin, da Jami’ar Koyarwa ta Calabar (UCTH) a Calabar.

An kaddamar da tallafin ne a watan Janairu a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

A cewar Hammatu Haruna Manaja mai kula da cibiyar Renal a asibitin koyarwa, ta ce tallafin zai kawo sauki ga marasa lafiya, inda ta kara da cewa kafin tallafin, majinyata da yawa na kokawa wajen samun damar yin wankin ƙoda.

Zuwa yanzu tun daga ranar 8 ga Janairun 2025, marasa lafiya 35 sun ci gajiyar shirin, har ma ta yabawa ma’aikatar lafiya ta tarayya da ta samar da isassun kayan aiki da suka hada da injin wankin ƙoda guda daya da kuma na’urar wankin sama da 900 domin tabbatar da nasarar shirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here