Tinubu ya aika wasiƙa ga majalisar Dattawa, yana neman ta tabbatar da Aminu Dalhatu da sauran mutane Biyu a matsayin Jakadu

Bola Tinubu Teacher 750x430

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa da wasiƙa yana neman a tantance sannan a tabbatar da sunayen wasu mutane uku da aka zaɓa domin zama jakadu a ƙasashen waje.

Sunayen da aka gabatar sun haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke daga Jihar Oyo.

Majalisar ta karanta wasiƙar a zauren majalisa yayin zaman bangaren ta hannun Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an yi zaɓen ne bisa tanadin kundin tsarin mulki na 1999, sashe na 171 (1), (2)(c) da (4) da aka yiwa gyara.

Ya bukaci majalisar da ta gaggauta duba sunayen tare da tabbatar da su cikin lokaci, yana mai mika gaisuwa da girmamawa ga ’yan majalisar.

Daga nan Akpabio ya mika sunayen ga kwamitin hulɗa da ƙasashen waje da Sanata Sani Bello ke jagoranta domin tantance su tare da gabatar da rahoto cikin mako guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here