Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ƙi amincewa da dokoki biyu da majalisar tarayya ta amince da su kwanan nan.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa dokokin da shugaban ƙasa ya ƙi amincewa da su su ne dokar kafa cibiyar fasahar sufuri ta Najeriya ta shekarar 2025 da kuma dokar gyaran kafa Asusun amintattun ɗakunan karatu na ƙasa ta shekarar 2025.
Tinubu ya bayyana matsayinsa ne a cikin wasiku biyu da ya aika wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, waɗanda aka karanta a zaman majalisar a ranar Talata.
A cikin wasikar da ta shafi dokar kafa cibiyar fasahar sufuri ta ƙasa, shugaban ƙasa ya ce dokar ta kunshi kura-kurai masu tsanani da za su iya kawo matsala ga tsarin kuɗi na gwamnati.
Ya bayyana cewa sashe na 18 na dokar ya ba cibiyar damar karɓar kaso ɗaya cikin ɗari na kuɗin kaya da ake shigo da su ko fitar da su daga ƙasa ba tare da amincewar gwamnati ba.
Karanta: Da Ɗumi-Ɗumi: Farfesa Yakubu ya mika ragamar hukumar INEC ga shugabar riƙon ƙwarya
Haka kuma, ya nuna rashin amincewa da tanadin da ke bai wa cibiyar ikon karɓar rance ko ajiyar ba tare da amincewar shugaban ƙasa ba, sai dai idan adadin ya haura naira miliyan 50.
Tinubu ya ce wannan ya saba da dokar da ake amfani da ita a halin yanzu wadda ke buƙatar amincewar shugaban ƙasa kafin a ɗauki kowanne irin bashi, kuma cire wannan sharadi na iya janyo cin zarafi a harkokin kuɗi.
Shugaban ƙasa ya kuma soki tanadin da ke bai wa cibiyar damar saka jari da kuɗaɗen da suka wuce buƙata, yana mai cewa cibiyoyi da gwamnati ke biya daga kasafin kuɗi ba sa samun kuɗaɗen da za su yi irin wannan saka jari. Ya ce wannan tanadi na iya haifar da karkatar da kuɗaɗe daga asalin manufarsu.
Game da dokar Asusun amintattun ɗakunan karatu ta ƙasa, Tinubu ya bayyana cewa tana cike da rashin daidaituwa da wasu dokoki da manufofin gwamnati.
Ya ce sabuwar dokar ta sabawa manufofi kan yadda ake biyan ma’aikata, batun haraji, tsarin albashi da iyaka na shekaru da wa’adin aiki ga ma’aikatan gwamnati.
Shugaban ƙasa ya gargadi cewa amincewa da dokar a irin wannan tsari zai haifar da matsala ga manufofin gwamnati kuma zai sa a kafa sabon misali da bai dace da moriyar jama’a ba.
Da yake mayar da martani, shugaban majalisar dattawa Sanata Akpabio ya yaba wa Tinubu bisa irin kulawar da ya nuna wajen nazarin dukkan dokoki kafin amincewa da su, yana mai cewa majalisar za ta yi la’akari da dukkan shawarwarin da shugaban ƙasa ya bayar.













































