Tinubu da Trump za su gana kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya – fadar shugaban ƙasa

Tinubu and Trump

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump za su gana nan gaba don tattauna batun zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Bwala ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan maganganun Trump da suka zargi gwamnatin Najeriya da rashin ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kaiwa kan Kiristoci.

Ya ce shugabannin biyu suna da ra’ayi ɗaya wajen yaki da ta’addanci da tarzoma, inda ya ƙara da cewa gwamnatin Amurka a lokacin Trump ta tallafa wa Najeriya ta hanyar sayar da makamai.

Bwala ya bayyana cewa shugaban ƙasa Tinubu ya yi amfani da wannan dama wajen ƙara karfafa yaki da ta’addanci wanda ya samar da gagarumar nasara.

Karin labari: Shugaban Amurka ya yi barazanar ƙaddamar da hari a Najeriya sakamakon zargin kisan Kiristoci

Haka kuma, ya ce za a tattauna bambancin fahimta game da ko ‘yan ta’adda a Najeriya na kai hari ne ga Kiristoci kaɗai ko kuma ga mutane na addinai daban-daban yayin taron da ake sa ran gudanarwa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ko a fadar White House da ke Washington.

A gefe guda kuma, wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi gargadin cewa dole Najeriya ta ɗauki mataki kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci, inda ya ce gwamnatin Amurka ba za ta ci gaba da yin shiru kan lamarin ba.

A ranar Asabar, Trump ya bayyana cewa ya umurci ma’aikatar tsaron Amurka da ta fara shirin yiwuwar kai farmaki a Najeriya bisa hujjar cewa gwamnati ta kasa dakatar da kisan Kiristoci.

Wannan na zuwa ne bayan ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai “damuwa ta musamman” saboda zargin cin zarafin Kiristoci, abin da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karyata yana mai cewa hakan ba ya nuna hakikanin yanayin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here