Tattaunawar sulhu da zaman lafiya da ‘yan ta’adda ta kai ga sako sama da mutane 120 da aka yi garkuwa da su a Arewa maso Yamma, amma wai rahotanni na cewaa an sake yin garkuwa da wasu mutanen.
Yankunan Arewa maso Yamma a ƙasar nan sun shaida abubuwan tsaro masu rikitarwa yayin da shugabannin ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara da Katsina suka saki fiye da mutane 120, sai dai an samu rahoton sabon satar mutane da dama wanda ya faru a Zamfara.
PRNigeria ta rawaito cewa shahararren shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji ya saki sama da mutane 100 a Zamfara, yayin da wani da ba a san sunansa ba ya saki fiye da mutane 20 a Katsina.
Wadannan sakin mutanen sun biyo bayan tattaunawa da kokarin gina aminci da aka gudanar ta hanyar shirin “North West Operation Safe Corridor” na sulhun yankin.
Sai dai wannan cigaba mai kyau ya ruguje nan da nan saboda wani sabon hari da ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan Buzugu da Rayau a karamar hukumar Bukkuyum ta Zamfara, inda rahotanni ke nuna cewa an sace fiye da mutane 70.
An kai wadanda aka saki a Zamfara da Katsina zuwa asibitoci domin samun kulawa kafin a mayar da su ga iyalansu.
Hukumomi sun tabbatar cewa tsarin sulhun da ake gudanarwa ana sanya idanu sosai don tabbatar da sahihancinsa da hana kowace kungiyar yin amfani da tattaunawar don sake samun makamai ko sake aikatawa.
Halin rashin tsaro da rashin tabbas, da kuma sakin mutane da sabon satar su, na nuna irin kalubalen tsaro da hadaddun matsaloli da shirin sulhun yankin ke fuskanta.