Tattalin arziƙin Najeriya ya fi muni a yanzu fiye da yadda yake a shekarun 1960 – Masanin tattalin arziƙi

WhatsApp Image 2025 10 10 at 21.43.46 750x430

Wani masanin tattalin arziƙi daga Sashen Tattalin Arziƙi na Jami’ar North West Kano, Dakta Abdurrazaq Ibrahim Fagge, ya bayyana damuwa kan halin da tattalin arziƙin Najeriya ke ciki a yanzu, yana cewa ya fi muni fiye da yadda yake a shekarun 1960 duk da shekarun da aka kwashe ana samun kudaden ta fannin mai da aiwatar da gyare-gyare.

A cewarsa, tun bayan samun ‘yancin kai, tattalin arziƙin Najeriya yake samun koma baya, inda aka koma daga tattalin arzikin noma zuwa dogaro da mai, wanda a halin yanzu ke samar da fiye da kashi 70 cikin ɗari na kudaden musayar ƙasa.

Ya bayyana cewa a shekarun 1960, noma ne ke samar da fiye da kashi 85 cikin ɗari na kudaden shigar ƙasa da sama da kashi 80 cikin ɗari na ayyukan yi.

Sai dai fashewar arzikin mai a shekarun 1970 ta sa aka manta da noma, abin da ya sa ƙasar ta zama mai rauni ga sauye-sauyen farashin mai a duniya.

Karin labari: Jihar Kano da ƙananan hukumomi sun karɓi naira biliyan 348.2 daga asusun FAAC cikin watanni takwas

Dakta Fagge ya ce ƙarancin kudaden shiga da rikicin tattalin arziƙi da aka fuskanta a ƙarshen shekarun 1970 ya haifar da koma baya da hauhawar farashi, inda dogaro da mai ya jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin matsalolin har yanzu.

Ya kuma bayyana cewa shirin gyaran tsarin tattalin arziƙi (SAP) da gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta gabatar ƙarƙashin jagorancin Asusun Ba da Lamuni na Duniya da Babban Bankin Duniya a shekarun 1980 ya zama babbar mahanga, amma ya ƙara janyo rufe masana’antu, karuwar rashin aikin yi da talauci.

A cewarsa, bayan dawo da mulkin dimokuraɗiyya a 1999, gwamnatin Olusegun Obasanjo ta gudanar da wasu gyare-gyaren kudi da suka taimaka wajen samun yafiyar bashi da karuwar ci gaban tattalin arziƙi tsakanin 2000 zuwa 2010.

Sai dai ya ce wannan ci gaban bai daɗe ba saboda rikicin tattalin arziƙi na duniya da ya faru a 2007–2008, wanda ya sa Najeriya ta fara sake cin bashi har zuwa yanzu da bashin waje ya kai sama da dala biliyan 40.

Masanin ya ƙara da cewa adadin talauci a ƙasar ya karu daga kashi 40 cikin ɗari a 2018 zuwa kashi 63 cikin ɗari a 2025, yayin da matsalar rashin isasshen wutar lantarki ke kara dagula tattalin arziki.

Ya kuma bayyana cewa ƙasar na buƙatar megawatt 14,000 na wuta amma ana samar da kimanin megawatt 6,000 kacal.

Dakta Fagge ya kuma zargi hukumomin gwamnati da ɓoye gaskiyar alkaluman tattalin arziƙi don nuna kamar ana samun ci gaba alhali kuwa akasin haka ne.

Ya kammala da cewa duk da ƙananan nasarorin da aka samu a wasu fannoni, Najeriya ta fi samun daidaito da wadata a shekarun 1960 fiye da yadda take yanzu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here