Tattalin arziƙin Najeriya ya bunƙasa – NBS

Double digit GDP growth 750x430

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa, wato NBS, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 3.46 a rubu’i na uku na wannan shekarar ta 2024.

Wannan nasarar ta samu ne a cikin sauri idan aka kwatanta da rubu’i biyu na farko a shekarar ta 2024, kamar yadda rahoton NBS ya nuna.

Sai dai duk da bunƙasar ta tattazlin arzikin, wato kashi 3.19 a rubu’i na biyu, da 2.98 a rubu’i na farko, har yanzu ba a kai ga samun nasarar bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da kashi 6 ba kamar yadda gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi alƙawari.

Nasarar da aka samu ba ta rasa nasaba da ci gaban da aka samu a ɓangaren harkokin tattalin arziki da suka shafi bankuna da intanet, wanda ya inganta tattalin arzikin ƙasar da kashi 50 a tsakanin Yuli da Satumba.

Wasu matakan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka a makonsa na farko a mulki sun sa an yi tunanin zai bunƙasa tare da inganta tattalin arzikin ƙasar, wada ita ce mafi girman tattalin arzikin nahiyar.

Amma bayan wata 18 da fara mulkin, manyan matakan da ya ɗauka – cire tallafin man fetur da karya darajar naira – sun jawo tsadar rayuwa da aka daɗe ba a gani ba a ƙasar a cikin shekaru masu yawa, amma har yanzu ba a fara gani a ƙasa ba.

Ɓangaren man fetur na ƙasar, wanda shi ne kan gaba wajen samar da kuɗin shiga ga gwamnatin ƙasar, ya samu bunƙasa da kashi 5.17, inda gangar man da ake fitarwa a ƙasar ya ƙaru zuwa ganga miliyan 1.47 a rana, maimakon ganga miliyan 1.41 da ake fitarwa a rubu’i na biyu na shekarar.

An samu koma-baya ne a ɓangaren noma daga kashi 1.41 a rubu’i na biyu, zuwa 1.14 a rubu’i na ukun, sannan ɓangaren masana’antu ya samu tagomashi daga 2.18 zuwa 3.35 a watan Afrilu zuwa Yuni.

Bankin bayar da lamuni ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai haɓaka da kashi 2.9 a shekarar 2024, da kuma 3.2 a shekara mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here