Taron dangi aka yi mun na faɗi zaɓe a majalisa – Abdulaziz Yari

0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata a Majalisar dattijai ta Najeriya, ya yi ikirarin cewa taron dangi aka yi masa, aka kayar da shi a takarar da yan yi ta neman shugabancin majalisar dattijai ta 10.

Sanata Abdulaziz Yari ya shaida wa BBC cewa zaɓen ya zo masa da mamaki saboda har zuwa lokacin da aka kai ga zaɓen yana da kwarin guiwar samun nasara.

Sai dai duk da haka sanatan ya ce ya amince da shan kaye.

“Zaben majalisa, ba zaɓe bane da ake yi wa jayayya a ce ko an yi maguɗi, babu magudi a cikinsa, mu 109 ne kuma kowa zai zo da ra’ayinsa, da abinda hankalinsa ya ba sa ya yi, kuma sun yanke hukunci”.

Sanatan ya kuma ce da ya san ba zai ci zaɓen ba tun farko da bai tsaya takarar neman shugabancin majalisar dattijan ba.

Ya yi ikirarin cewa a ranar da su fara daukar sakamako na mutanen da ke mara masa baya sun samu adadi da zai sa su iya samu rinyaje a zaɓen.

Sai dai ya yi zargin cewa taron dangin da aka yi masa ya sa ya sha kaye.

“Shugaban kasa na ciki, mataimakin shugaban kasa na ciki, haka sakataren gwamnati na ciki da gwamanoni, ni kadai ne sai waɗannan bayin Allah.”

“Ina fatan gobe idan shugaban kasa ya dawo a karo na biyu, zai yarda dimukuruɗiyya ta dauki matakinta a cikin majalisa, ya ce yana son wane amma abin adalci ga shugaba shi ne da wannan da wannan duka na kane,” in ji shi.

Sai dai duk da korafe -korafen da sanatan ya yi, ya ce dangantakar da ke tsakaninsa da shugaba Bola Tinubu ba ta sauya ba saboda ya rungumi kaddara.

“Na dauka Allah ne ya yi, ban dauka Tinubu ne ya yi ba, Allah ne ya yi, domin Allah ne ya kaddara cewa zai zamo,”in ji Yari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here