Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana zaɓen Gwamna na ranar Asabar a matsayin mafi tsari da inganci da hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta gudanar a jihar zuwa yanzu.
Soludo ya bayyana hakan ne a jawabinsa na nasara da ya gabatar a garin Awka ranar Lahadi, bayan hukumar ta zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 8 ga watan Nuwamba.
Shugaban jami’ar Benin, Farfesa Edoba Omoregie, wanda shi ne jami’in tattara sakamakon, ya sanar da cewa Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ya samu kuri’u 422,664, inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Cif Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 99,445.
Karanta: INEC ta bayyana Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Gwamnan jihar Anambra
Soludo ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da sahihin zaɓe a jihar, tare da yabawa sabon shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Joash Amupitan, da ya jagoranci gudanar da zaɓen cikin nasara.
Ya kuma jinjinawa sashen fasahar sadarwa na hukumar zaɓe bisa tabbatar da gaskiya da nunata a fili ta hanyar ɗora sakamakon rumfunan zaɓe kai tsaye a shafin IReV, inda kashi 99 cikin 100 na sakamakon aka ɗora cikin dare.
Gwamnan ya kuma taya sauran ‘yan takara murna, yana mai cewa siyasar jihar Anambra ya kamata ta kasance ta gasa ta ra’ayoyi ne, ba ta gaba da adawa ba, tare da bayyana shirinsa na yin aiki tare da kowa domin ci gaban jihar.
Soludo ya bayyana nasararsa a matsayin amanar tarihi daga mutanen Anambra, inda ya ce wannan lokaci ne da al’umma suka nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnatinsa, kuma za su ci gaba da ganin an kawo ci gaba da walwala ga jihar.












































