Wani iftila’i ya afku a jihar Sokoto bayan wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Shagari, inda ake fargabar fasinjoji da dama sun bace a ruwa.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Ahmed Aliyu a hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Sokoto SEMA Aminu Bodinga, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Juma’a.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, ya na mai cewa, an aike da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar zuwa inda hatsarin ya afku domin bincike da ceto mutanen da hatsarin ya ritsa da su.
A cewarsa, jami’an SEMA suna aiki tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta NIWA domin ceto wadanda suka tsira da rayukansu da kuma ceto wadanda suka jikkata.
Bodinga ya ce, kwale-kwalen da ke cikin halin rashin ingancin lafiya na dauke da fasinjoji da dama a lokacin da ya kife, da mutanen ciki baki ɗaya.
Sai dai mai taimaka wa gwamnan ya kasa bayar da alkaluman adadin wadanda suka mutu, amma mazauna yankin sun nuna fargabar cewa yawancin fasinjojin da ke cikin jirgin ba za su tsira daga hatsarin ba.
A lokacin gabatar da wannan rahoto, jami’an SEMA na aiki tare da NEMA da NIWA wajen gudanar da ayyukan ceto.
Hatsarin na baya-bayan nan ya faru ne kasa da mako biyu bayan wani hatsarin kwale-kwale a jihar ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla uku tare da bacewar wasu sama da 20.
An ce wadanda lamarin ya rutsa da mutanen ne yayin da suke kokarin tsallaka kogin a lokacin da kwalekwalen ya kife da su.













































