Sojojin ruwan Maroko sun ceto bakin haure 141 ‘yan Afirka da ke cikin kwale-kwale da suka gamu da matsala yayin da suke tafiya daga Mauritania zuwa tsibirin Canary na Spain.
An ceto mutanen ne a ranar Lahadi, kimanin kilomita 274 kudu maso yammacin Dakhla a cikin hamadar yammacin sahara.
Karanta wannan: Kamfanin X ya amince zai biya tsoffin ma’aikatansa na Ghana
‘Yan baƙin hauren sun tashi ne daga gabar tekun Mauritania a ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda rahotanni daga sojojin ruwan Morocco suka rawaito.
A bara, tsibirin Canary ya dauki kusan baƙin haure 32,000, wanda ya zama mafi yawan adadin da aka samu tun shekara ta 2006.
A watan Janairu, hukumomin Spain sun ba da rahoton ci gaba da ƙaruwar bakin haure zuwa tsibiran, inda aƙasarin jiragen ruwa suka fito daga Mauritania.