Sojoji sun kama taki, magunguna da na’urorin hasken rana da ake nufi kai su ga ƴan ta’adda a Yobe

IMG 20250919 WA0005 606x430

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas Operation HADIN KAI (OPHK) sun cafke wata babbar tirela dauke da kayan tallafin da ake zargin an tanadar wa ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Mai magana da yawun OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba, ya ce an samu wannan nasara ne a ranar 16 ga Satumba lokacin da sojoji ke binciken gaggawa a kan hanyar Nguru zuwa Gashua a Jihar Yobe.

Ya bayyana cewa sojojin Operation DESERT SANITY IV ne suka tsaida tirela mai tayoyi 14 da karfe 7:40 na safe, inda daga bisani aka kaita wuri mai tsaro aka duba.

Karin labari: Harin Borno: Tinubu ya umurci sojoji su sake duba tsare-tsaren yaƙi da Ta’addanci

A cewar Uba, bincike ya gano buhunan taki NPK 20:10:10 guda 700, kwalaye 27 na magunguna iri daban-daban da kwalaye 9 na ruwan asibiti da aka ɓoye a ƙarƙashin kaya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa dakarun soji sun sha bayyana taki a matsayin muhimmin kayan haɗa bama-baman IED.

Uba ya ƙara da cewa kayan da aka kama an nufa da su ne zuwa Jamhuriyar Nijar, kuma ana zargin suna cikin hanyar samar da kayan abinci da makamai ga ’yan ta’adda a kan iyaka.

Ya ce an kuma cafke wata tirela da motoci biyu kirar Toyota Sharon dauke da kaya da kuma na’urorin hasken rana.

Bisa ga bayanan leken asiri, Uba ya ce kayan sun haɗa da masana’antu da ake amfani da su wajen kera kayan sanye da na’urorin aiki ga ’yan ta’adda.

Dukkan direbobi da matasan mota tare da kayayyakin da aka kama suna hannun dakarun soji yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka turo da kayan.

Laftanal Kanal Uba ya bayyana cewa kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya jinjinawa dakarun bisa ƙwazon su.

Ya kuma tabbatar da cewa za a ci gaba da karya duk wata hanyar samar da kayan aiki ga ’yan ta’adda tare da kira ga jama’a su rika ba da bayanai cikin gaggawa domin taimaka wa ayyukan tsaro.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here