Sojojin Najeriya sun kama wanda ake zargin dillalin makamai ne, sun kuma ceto wani da aka sace, tare da tarwatsa hanyoyin jigilar kayan ta’addanci cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Majiyar da ta fito daga babban ofishin rundunar sojoji ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa sojojin aikin FANSAN YAMMA sun kama wani da ake zargin mai bai wa ’yan ta’adda bayanai ne a Ungwan Gombawa da ke karamar hukumar Kontagora ta jihar Niger.
Majiyar ta ce sojojin Birigediya ta 1 sun kuma kama wani da ake zargin babban mai samar da kayan aiki da makamai ga ’yan ta’adda a Danjigba da ke karamar hukumar Bukkuyum.
Binciken farko ya nuna cewa yana da alaƙa da wasu mutane biyu da ke ajiye makamai da ake shigo da su daga jamhuriyar Nijar a karamar hukumar Anka.
Yayin binciken an samu kayan sojan da suka hada da riguna, hula, takalma, da takardun kudade da suka kai kusan Naira Miliyan Hudu, da kuma sautin bayanan tattaunawar makamai.
Haka kuma, sojojin da ke bin sahun wadanda suka sace daliban makarantar GGSS Maga da ke jihar Kebbi sun mamaye sansanin wani shugaban ’yan ta’adda mai suna Bello Kaura a dajin Gando–Sunke, inda ’yan ta’addan suka gudu suka bar wurin, sojoji kuma suka tarwatsa sansanin baki ɗaya.
A wani samamen, sojoji sun kama wani mutum da ake zargin mai kai bayanai ne daga Sokoto a yankin Augie, inda suka samu katunan ATM guda biyar, kaya da kuma Naira Dubu Saba’in da Tara.
A jihar Katsina kuma sojojin sun tsira daga wani kwanton bauna a hanyar Kaiga–Mara, lamarin da ya sa maharan suka tsere.
Wasu ayyuka a yankunan Shinkafi da Zurmi sun haifar da musayar wuta, inda sojojin suka kama bindigogin AK-47 guda biyu, alburusai da babura guda biyu.
A karkashin aikin Enduring Peace da ake aiwatarwa a jihar Plateau, sojoji sun hana wani yunkurin sace mutum a Jos Kudu, inda aka ceto wanda aka yi garkuwa da shi, duk da cewa ya samu raunin harbin bindiga.
Karin labari: Matsalolin Tsaro: Jihohon Katsina da Plateau sun umarci a rufe makarantu nan take
A wani samame daban a wurin, an kama wasu makiyaya takwas da ake zargin masu aikata laifi ne.
Majiyar ta kara da cewa sojojin aikin Whirl Stroke sun amsa kiran gaggawa kan wani hari a Nasarawa, inda aka sace fasinjoji uku yayin da direban ya ji rauni, kuma ana ci gaba da kokarin ceto su.
Haka nan, an kama wasu makiyaya biyu da ake zargin suna lalata amfanin gona a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyarar aiki jihohin Borno, Kaduna da Zamfara domin duba yadda ayyukan yaki da ta’addanci ke gudana tare da karfafa gwiwar sojoji kan muhimmancin kiyaye ka’idoji da shiri a fagen fama.













































