Sojojin haɗin gwiwa na rundunar Operation MESA da ke ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano sun yi nasarar dakile harin ‘yan bindiga tare da kare al’ummomin yankin daga kai musu farmaki.
Bisa bayanin da Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Runduna ta 3 ta sojojin Najeriya, ya fitar, ya ce rundunar ta samu bayanan sirri kan motsin ‘yan bindiga a yankunan Unguwar Tudu, Unguwar Tsamiya da Goron Dutse da ke Shanono, inda nan take suka kaddamar da samame a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 5 na yamma.
Ya bayyana cewa sojojin tare da sauran jami’an tsaro sun gwabza da ‘yan bindigar a faɗa mai zafi, wanda hakan ya sa suka gudu bayan sun yi asarar mutane da dama.
Haka kuma ya ce ‘yan bindigar sun iso yankin ne da babura, inda daga bisani aka kwato wasu babura da wayoyi guda biyu bayan fafatawar.
A cewar Zubairu, ‘yan bindiga 19 ne aka hallaka a harin, yayin da sojoji biyu da ɗan sa-kai ɗaya suka rasa rayukansu.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankunan domin tabbatar da kariyar al’umma daga hare-haren ‘yan bindiga da satar shanu da sauran laifuffuka.
Kwamandan Runduna ta 3 ta sojojin Najeriya, Birgediya Janar Ahmed Tukur, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa sojojin za su ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.













































