Sojoji sun ƙi karɓar cin Hancin fiye da Miliyan 13 daga ƴan bindiga

Army keeps peace in Kaduna

Shalkwatar tsaron Najeriya, ta ce dakarun Operation Safe Haven sun ki amincewa da karɓar cin Hancin Naira miliyan 13 da dubu 700 da ƴan ta’adda suka bayar a wani samame da suka kai a hanyar Jos zuwa Sanga a Filato.

Daraktan yada labarai na shalkwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kanye, ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai kan ayyukan da sojoji suka yi a fadin Najeriya Alhamis yau Alhamis a Abuja.

Kangye ya ce, sojojin sun amsa kiraye-kirayen da aka yi musu ne game da ayyukan ta’addanci a lokacin da suka kama wasu ‘yan ta’adda biyu da suka yi yunkurin ba su cin hancin Naira miliyan 13 da dubu 700.

Ya ƙara da cewa sojojin sun kuma kai farmaki tare da amsa kiraye-kirayen kai ɗauki a ƙananan hukumomin Bassa da Barkin Ladi da South Wase da Riyom da Jos East Duke a Jihar ta Filato.

A cewarsa, haka zalika sojojin sun kai farmaki a ƙananan hukumomin Kaura da Sanga na jihar Kaduna.

Ya ce a yayin samamen, sojojin sun yi artabu da ƴan ta’adda inda suka kashe wasu, suka kama mutane 12 da ake zargi tare da kubutar da mutane uku da aka yi garkuwa da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here