Sojin Mozambik sun daƙile yunƙurin ɗaukar ma’aikata tsageru

Sojojin, Mozambik, ma'aikata, tsageru, yunkuri, daukar, dakile
A jiya ne shugaban ƙasar Mozambique Filipe Nyusi ya sanar da cewa sojojin kasar sun dakile yunƙurin da masu tayar da ƙayar baya suka yi na daukar ma'aikata...

A ranar Laraba ne shugaban ƙasar Mozambique Filipe Nyusi ya sanar da cewa sojojin kasar sun dakile yunƙurin da masu tayar da ƙayar baya suka yi na daukar ma’aikata yara kanana a gundumar Chiure da ke arewacin kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai bayan wani zama da manyan jami’an gwamnatin lardin Cabo Delgado.

Ya ce masu tayar da ƙayar bayan sun koma yankunan kudancin lardin Cabo Delgado ne domin daukar matasa aikinsu.

Karin labari: Gwamnati za ta ƙara yawan mutanen da za ta baiwa tallafin kuɗi

“A gaskiya, dole a yi tsammanin rikicin Ocua saboda suna son ɗaukar yara aikin ta’addanci,” in ji Nyusi.

Yankin ya sami ƙaruwar ayyukan tsageru a ‘yan makonnin nan, inda kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka danganta shi da wani kamfen na kashe su a duk inda aka same su da kungiyar IS ta kaddamar a ranar 4 ga watan Janairu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here