Shugabannin mulkin soji a Nijar sun naɗa ministoci

Ali Mahaman Lamine Zeine
Ali Mahaman Lamine Zeine

Shugabannin mulkin soji a Nijar sun sanar da naɗa ministoci. Sojojin sun sanar da haka ne a wata doka da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar a cikin dare.

Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine shi zai jagoranci mambobi 21 na gwamnatin, inda sabbin janar-janar ɗin gwamnatin mulkin sojin za su shugabanci ɓangaren tsaro da kuma harkokin cikin gida.

Hakan na zuwa ne yayin da ECOWAS ke gudanar da taro yau Alhamis a Abuja domin yiwuwar ɗaukar matakin soja ko bin hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin na Nijar.

Tun da farko sojojin na Nijar sun yi watsi da wa’adin da ECOWAS ta ba su na mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here