Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya kaddamar da wani kwamiti na wucin gadi domin duba tasirin tattalin arziki, tsaro da dokokin da suka shafi harkokin kudin intanet (cryptocurrency) da na’urar biyan kuɗi ta POS a ƙasar nan.
An kaddamar da kwamitin ne a Abuja, inda Tajudeen ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda yawaitar damfara, laifukan internet da cin zarafin masu amfani da fasahar kuɗin zamani a ƙasar.
Ya ce duk da cewa tattalin arzikin Najeriya ya nuna ƙarfi wajen murmurewa daga matsin lamba da kuma bunƙasa a wasu fannoni, akwai bukatar kulawa da yadda ake mu’amala da kuɗin intanet.
Shugaban ya bayyana cewa duk da fa’idar kuɗin intanet wajen haɓaka kasuwanci, akwai barazana daga ɓangaren safarar kuɗi ta haram, tallafa wa ta’addanci da rashin bin ƙa’idoji.
Saboda haka, majalisar ta ga dacewar kafa tsarin doka da zai tabbatar da kariyar jama’a da tsabtace ayyukan masu harkar kuɗin intanet da sauran kudade na zamani.
Tajudeen ya ce, aikin kwamitin zai haɗa da sauraron ra’ayoyin jama’a da na hukumomi domin tattara bayanan da za su taimaka wajen samar da tsarin doka mai inganci da kuma taimakawa majalisar wajen sa ido kan amfani da kuɗin internet a Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa majalisa ta 10 tana tsayawa kan kare ƙasar daga duk wani abin da zai iya kawo cikas ga gyaran tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi.
Ya roƙi mambobin kwamitin su kasance masu kishin ƙasa a yayin gudanar da aikinsu.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Hon. Olufemi Bamisile daga Jihar Ekiti, ya ce aikin na da muhimmanci matuƙa, domin yana neman daidaita tsakanin ci gaban fasahar kuɗi da kuma tsaron ƙasa.
Ya bayyana cewa duk da cewa kuɗin intanet da POS suna sauƙaƙa harkokin kasuwanci da shigar jama’a cikin harkar kuɗi, suna kuma kawo barazana ta damfara da safarar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ƙara da cewa kwamitin zai yi aiki kafada da kafada da hukumomin CBN, SEC, NDIC, NFIU, EFCC, ICPC da rundunar ‘yan sanda domin samar da doka mai daidaito wacce za ta kare masu amfani da tsarin kuɗin zamani tare da tabbatar da amincin tsarin kuɗin ƙasa.
NAN













































