Shugaban Jami’ar KHAIRUN ya buƙaci kungiyar ɗalibai NANS ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaban kasa

588247318 839612592110162 3729519939483501914 n 750x430

Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano (KHAIRUN), Farfesa Abdulrasheed Garba, ya buƙaci kungiyar ɗalibai NANS ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaban kasa.

Farfesan ya yi wannan kira ne lokacin ziyarar ban-girma da ƙungiyar ta kai masa a ranar Talata a jami’ar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Riko na Hulɗa da Jama’a da Tallata Ayyuka na KHAIRUN, Bilal Dahiru Tijjani, ya fitar a ranar Laraba, an bayyana cewa shugaban jami’ar ya nemi ɗaliban su dinga kallon Najeriya ta fuskar irin gudummawar da za su iya bayarwa a matsayin ’yan ƙasa nagari.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an mika wa shugaban jami’ar shaidar girmamawa daga hannun ƙungiyar NANS.

Mataimakin Shugaban NANS na ƙasa, Kwamared Ahmad Abubakar Mallawa, ya yabawa jagorancin Farfesa Garba, yana nuna cewa wannan karramawa ta samo asali ne daga kwazon aikinsa da tasirinsa wajen ci gaban ilimi a ƙasar nan.

Ya ƙara da cewa ziyarar an yi ta ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙungiyar da jami’ar KHAIRUN, tare da yabon ɗaliban jami’ar bisa ɗa’a da tarbiyya.

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulrasheed Garba, ya nuna godiyarsa ga NANS bisa wannan karramawa, sannan ya bayyana wa tawagar hangen nesa da ka’idoji da ci gaban da jami’ar ta samu zuwa yanzu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here