Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da daukar wasu matasa yan hidimar kasa su 200 aiki wadanda suka samu lambar yabo ta shugaban kasa inda ya umarci a basu shaidar daukar aiki a gwamnatin tarayya cikin gaggawa tare da ba su kyautar kudi Naira 250,000 da kuma tallafin karatun digiri na biyu ga kowane.
Shugaban ya kuma sanar da daukar tsoffin ‘yan hidimar kasar mutum 10 wadanda zama masu bukata ta musamman yayin da suke gudanar da aikin hidimar kasar sakamakon raunukan da suka samu inda ya bayyana su a matsayin jarumai da ba za a taba mantawa da irin sadaukarwar da suka yi ba.
Da yake magana ta bakin Karamin Ministan Kwadago da samar da aiki, Nkeiruka Onyejeocha, a wajen taron karrama yan hidimar kasar na shekarun 2020-2023 da aka gudanar a Abuja, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, matakin ya nuna irin kudirin gwamnati na ci gaban matasa da yi wa kasa hidima.
Haka kuma, ya yaba wa wadanda aka karraman saboda kishin kasa da nuna da’a da rashin son kai, da da hakan ya sanya su kasancewa abun koyi, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da suka yi na da matukar muhimmanci ga hadin kan al’ummar kasar nan da kuma ci gaban kasa mai dorewa.
“A saboda godiya da hidimar da suke yi wa kasa, duk wadanda aka karrama za su samu Naira 250,000, kuma za a ba duk wanda ya samu lambar yabo guraben karatu don ci gaba da karatun digiri har zuwa matakin Digiri na uku watau PhD a kowace jami’a a kasar,” in ji Tinubu.
Shugaban ya bayyana cewa, gwamnatin ta bullo da wasu tsare-tsare da suka shafi matasa a fannonin ilimi da bunkasa sana’o’i da fannin fasaha da kuma sana’o’in hannu domin samun damar yin amfani da damar ga matasan Najeriya.













































