Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Samar da Abinci a Najeriya 

Bola Tinubu sabo sabo.jpeg
Bola Tinubu sabo sabo.jpeg

Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana ta ɓaci kan tsamar da isasshen abinci a Najeriya. Kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake ne ya bayyana haka yayin zantawa da masu ɗauko rahoton gidan gwamnati ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, 2023.

Shugaban kasan ya bada umarnin cewa duk wasu batutuwa da suka shafi abinci da samar da ruwan sha da sauke farashi a maida su karkashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

Wannan umarni na cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na tabbatar da cewa talakawa masu karamin karfi suna iya dogaro da kansu.

Bugu da ƙari, shugaban kasan ya umarci a gaggauta fitar da takin zamani da hatsi a raba wa manoma da magidanta domin rage musu zafin raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Hadimin shugaban ƙasa, D. Olusegun ya wallafa cikakkiyar hirar shafinsa na Tuwita. Dele Alake ya ce: “Dole ma’aikatar noma da ma’aikatar ruwa su hanzarta haɗa kai wajen tabbatar da an samun isasshen ruwa a gonaki da kuma tabbatar da ana samar da abinci a kowane lokaci cikin shekara.”

“Zamu kirkiro da kuma goyon bayan hukumar kayyakin abinci wacce zata sa ido, nazari da kuma bibiyar farashin kayan abinci. Haka nan hukumar zata riƙa killace abinci da nufin amfani da su a matsayin makamin saita farashi.”

“Ta hannun wannan hukumar, gwamnati zata shiga ta yi ruwa da tsaki wajen saita tashi da saukar farashin kayayyakin abinci a Najeriya.” Haka zalika ya ƙara da cewa gwamnati zata shigo da hukumomin tsaro cikin batun abinci domin tsare gonaki da manoma ta yadda aikin noma zai kankama ba tare da tsoron hari ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here