Shugaba Tinubu na hanyar komawa Najeriya daga ƙasar Brazil

Tinubu depart US 750x430

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya baro birnin Brasíliya na kasar Brazil zuwa Abuja bayan kammala ziyarar aiki da ya kai da kuma karfafa alaka tsakanin Najeriya da kasar Brazil.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito, cewa jirgin shugaban kasan ya tashi ne daga sansanin sojojin sama na kasa da kasa na birnin Brasília da misalin karfe 12:57 na dare a agogon kasar ta Brazil.

Sakataren nahiyar Afrika da Gabas ta Tsakiya Ambasada Carlos Sérgio Sobral Duarte, da kuma jakadan Brazil a Najeriya Ambasada Carlos José Areias Moreno Garcete, sun halarci filin jirgin saman domin yin bankwana da shugaba Tinubu yayin tashin nasa.

Karamar ministar harkokin wajen kasar nan Bianca Odumegwu-Ojukwu da sauran jami’an gwamnatin kasar nan su ma sun kasance a filin jirgin.

Haka kuma yayi barin filin jirgin da shuga Tinubu ya yi wani jami’in tsaron kasar Kanal Cel Nicolas ya jagoranci yin faretin ban-girma ga shugaba Tinubu gabanin tasowar tasa.

Shugaban kasa, Tinubu ya isa birnin Brasília ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 25 ga watan nan da muke ciki na Agusta, domin gudanar da harkokin diflomasiyya.

Da isar shi, ya samu tarba da cikakkiyar girmamawa ta soja, kuma nan take ya gana da shugaban kasar Luiz Inácio Lula da Silva da manyan jami’an kasar Brazil.

Shugabannin biyu sun yi wata tattaunawa ta sirri tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda biyar.

Yarjejeniyar ta shafi harkokin sufurin jiragen sama da harkokin waje da kimiyya da fasaha da kuma muhimman bangarorin noma a cikin ajandar ci gaban Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here