Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci Mataimakin sa Kashim Shettima da ya ziyarci jihar Kebbi a ranar Laraba domin jajanta wa gwamnati da iyalan ’yan makaranta mata da aka sace daga makarantar sakandare ta Maga tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
Shettima zai yi jaje ga iyaye da masu kula da waɗanda aka sace, tare da nuna cewa gwamnati na aiki da gaggawa domin ganin an dawo da yaran cikin koshin lafiya.
Shugaban ƙasa ta bakin mai ba shi shawara kan bayani da dabarun yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya mika ta’aziyyarsa ga rundunar soji bisa mutuwar sojoji ciki har da Birgediya Janar Musa Uba, wanda ya rasu a yayin fafutukar yaƙi da ’yan ta’adda a jihar Borno.
Tinubu ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ’yan ta’adda suka katse karatun ’yan makaranta mata marasa laifi, tare da umartar hukumomin tsaro da su hanzarta dawo da yaran zuwa jihar Kebbi.
Tinubu ya yaba wa Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris bisa ƙoƙarin da aka yi domin hana sace yaran, duk da cewa barazanar tsaro ta sa an sace su daga makarantar kwana ta Maga, tare da kira ga al’ummomi a faɗin ƙasa su rika bayar da bayanai da za su taimaka wa jami’an tsaro.
Hare-haren sun faru ne bayan ƴan bindigar sun bar gidan ma’aikatan makarantar, inda mataimakin shugaban makarantar Hassan Makuku ya rasa ransa yayin ƙoƙarin kare ɗaliban.
Jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan Kebbi Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma jami’an ’yan sanda, sojoji da masu sa kai suna binciken dazukan da ke kusa domin ceto yaran.
Gwamna Idris ta bakin babban sakataren yada labarai Ahmed Idris, ya tura Mataimakin Gwamna Umar Tafida domin duba halin da ake ciki, yayin da gwamnan da yake wajen jihar ke ci gaba da karɓar rahotannin tsaro.












































