Shaguna 180 sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto

Gobara, sokoto, Shaguna, babbar kasuwar
Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna....

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.

Garba Muhammad Gwazi, shugaban ‘ƴan mashin reshen jihar ya shaidawa manema labarai cewa gobarar ta laƙume shaguna 180 na masu sayar da mashin.

A cewarsa, har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin nairori. Sai dai ya ce gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun kashe farar hula fiye da 100 a gabashin Burkina Faso

Ya bayyana cewa gobarar ba ta kai ga asarar rai ko jikkata ba.

Gwazi ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai musu ɗauki domin “kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba.” in ji shi.

Shi ma Honarabul Ibrahim Muhammad Giɗaɗo, mai baiwa gwamna shawara kan babbar kasuwar ya ce wutar ta tashi da sanyin safiyar yau.

Karin labari: Hukumar KNUPD ta rusa gidaje a unguwar Gurun Gawa

Ya ce “ɓangaren da ya ƙone sosai a cikin kasuwar shi ne na ‘ƴan mashin da kekuna, ana iya samun shago guda ɗauke da mashin fiye da 200 ko 100, shagunan gaba ɗaya sun ƙone, waɗannan mashina akwai waɗanda suka haura miliyan, akwai asara mai yawa.”

Giɗaɗo ya ƙara da cewa jami’an kashe gobara sun kashe kashi 80 cikin 100 na gobarar da ke ci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here