Sauya sheƙa: gwamnoni sune shugabannin jam’iyyar APC a jihohinsu – Tinubu

Bola Tinubu 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya jaddada cewa dukkan gwamnonin da ke ƙarƙashin jam’iyyar APC su ne shugabannin jam’iyyar a jihohin da suke jagoranta.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron karɓar Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, zuwa APC a birnin Jalingo, inda Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi, tare da sanar da cewa sauya sheƙar gwamnan daga PDP ya ba shi cikakken jagoranci na APC a jihar Taraba.

Shugaban ƙasar ya nuna aniyarsa ta goyon bayan gwamnan da majalisar zartarwarsa domin samar da ci gaba a Taraba, yana mai jaddada cewa gwamnan na ƙoƙarin haɗa kan al’ummar jihar tare da daidaita bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin cimma haɗin kai.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Taraba da su mara wa gwamnan baya domin ya samu nasara, tare da bayyana farin cikinsa kan sauya sheƙar gwamna daga yankin Arewa maso Gabas, yana ƙarfafa jihohin Adamawa da Bauchi da su shiga jam’iyyar da ke mulki a matakin tarayya.

A nasa ɓangaren, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yelwatda, ya yaba wa Agbu Kefas bisa jajircewarsa na sauya sheƙa zuwa APC, yana mai bayyana cewa ficewarsa daga PDP zuwa APC babban ci gaba ne da zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Taraba tare da bunƙasa damar matasa da mata.

Ya tabbatar wa mambobin APC na da da sabbi cewa za a ba su dama iri ɗaya a harkokin jam’iyyar, tare da shawarci gwamnan da ya haɗa kan jam’iyyar ba tare da nuna bambanci ba.

Yana mai bayyana cewa Taraba za ta zama cikakkiyar ɓangare ta jam’iyyar da ke da damar yin nasara a babban zaɓe mai zuwa.

A yayin jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibril, ya wakilta, ya taya al’ummar Taraba da gwamnan murna, yana mai cewa sauya sheƙar za ta kawo wa jihar fa’ida ta fuskar ci gaba, inganta ababen more rayuwa da ƙarfafa tsaro.

Shi ma Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa sauya sheƙar an yi ta ne domin makomar Taraba da muradun al’ummarta baki ɗaya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here