Jakadan Saudiyya a Birtaniya ya ce ƙasarsa tana sha’awar daidaita dangantaka da Isra’ila bayan kammala yaƙi a Gaza.
Yarima Khalid bin Bandar ya bayyana cewa ana daf da cimma yarjejeniya lokacin da Masarautar ta dakatar da tattaunawar da Amurka ta shiga tsakani bayan miyagun hare-haren da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktobar da ta gabata.
Karanta wannan: Kano: Sakataren gwamnatin jiha ya dawo daga hutun jinya a kasar Saudiyya
Sai dai har yanzu Saudiyya tana da imanin cewa ƙulla dangantaka da Isra’ila abu ne mai yiwuwa.
Jakadan ya kuma yi gargaɗin cewa akwai “gazawar jin ƙan ɗan’adam game da batun Gaza, inda al’ummar duniya ta kasa yin isasshen abin da ya dace don kawo ƙarshen yaƙin.
Saudiyya ita ce jagora ga ƙasashen Larabawa da kuma na Musulmin duniya, ba ta taɓa amincewa da Isra’ila ba a ƙa’idance, tun da aka kafa ta cikin 1948.
Karanta wannan: EFCC ta gurfanar da tsohon minista Olu Agunloye
Don haka duk wata yarjejeniyar ƙulla dangantaka za ta kasance wata gagarumar nasara ga ƙasar ta Yahudawa.
A ƙarshen watan Samtumba ne dai jagoran da ke riƙe da iko a Saudiyya ya ayyana yayin wata hira da aka yi da gidan talabijin na kasar Amurka suna dab da cimma wata yarjejejniya mai karfin gaske.