Saudiyya ta tsawaita zaman ƴan Sudan da suka je yin Umrah

Mecca
Mecca

Saudiyya ta ce ta yanke shawarar tsawaita bizar ƴan Sudan da suka je domin yin Umrah.

Saudiyyan ta kuma kaddamar da wani shiri da zai bai ƴan asalin ƙasar da kuma waɗanda ke zama a can, damar karɓar bakuncin ƴan Sudan bayan sauya bizarsu ta Umrah zuwa ta ziyara.

Matakin na zuwa ne bayan umarnin da Yarima Bin Salman ya bayar na yin haka wanda ke cikin ayyukan jin kai da suka ɗauka na tallafawa mutanen Sudan, a cewar kamfanin dillancin labaran Saudiyya.

Hukumar kula da fasfo a ƙasar (Jawazat), ta fara shirye-shiryen tsawaita bizar ƴan Sudan ɗin da suka je yin Umrah waɗanda kuma suka kasa komawa gida saboda faɗa da ake ci gaba da yi a ƙasarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here