Sarkin Kanwan Katsina ya yaba wa ƙungiyar NIPR kan rawar da take takawa wajen wayar da kai da bunƙasar ƙasa

WhatsApp Image 2025 10 12 at 08.47.08 750x430

Sarkin Kanwan Katsina kuma hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello Kankara, ya yaba wa ƙungiyar ƙwararrun masu hulɗa da jama’a ta Najeriya (NIPR) bisa irin rawar da take takawa wajen inganta wayar da kai da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Alhaji Ahmad Sajo, ɗan majalisar gudanarwa ta ƙungiyar NIPR, tare da sabbin shugabannin reshen ƙungiyar na jihar Katsina da suka kai masa ziyarar ban girma.

Ya bayyana cewa dawo da ayyukan ƙungiyar a jihar babban ci gaba ne da zai taimaka wajen ƙara ƙwarewar jami’an hulɗa da jama’a da ke aiki a fadin jihar.

Ya shawarci sabbin shugabannin ƙungiyar da su yi amfani da kafafen yada labarai na gargajiya da na zamani wajen ƙarfafa jami’an hulɗar jama’a su yi rijista da reshen ƙungiyar ta jihar Katsina, domin su zama ƙwararru bisa doka.

Wannan ya yi daidai da sabon tanadi da ke buƙatar cewa duk wanda zai riƙe mukamin jami’in hulɗar jama’a a ma’aikata ta gwamnati ko ta masu zaman kansu dole sai ya zama mamba na ƙungiyar NIPR.

Solacebase ta ruwaito cewa, Sarkin Kanwan Katsina ya bukaci a buɗe ofishin ƙungiyar a jihar domin tabbatar da ingantaccen aiki, tare da yin alƙawarin goyon baya ga ƙungiyar.

Sarkin ya kuma tuna cewa ya taɓa yin aiki a tashar rediyo ta tarayya (FRCN) Kaduna a matsayin ɗan jarida, sannan daga baya ya riƙe mukamin jami’in hulɗar jama’a na hukumar kwastam a Apapa da Tincan Island har tsawon shekaru goma.

A shekara ta 1999 kuma ya lashe lambar yabo ta mafi ƙwararren jami’in hulɗar jama’a a hukumar kwastam ta Najeriya a taron shekara-shekara da aka gudanar a birnin Fatakwal.

A nasa jawabin, Alhaji Ahmad Sajo ya bayyana cewa zuwansa jihar Katsina yana wakiltar shugaban ƙasa na ƙungiyar NIPR, Dakta Ike Neliaku, domin kaddamar da sabbin shugabannin reshen ƙungiyar na jihar.

Ya gode wa Sarkin Kanwan Katsina bisa goyon bayansa ga ‘yan jarida da masu hulɗar jama’a, tare da bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin farkon ‘yan asalin jihar Katsina da suka fara zama mambobin ƙungiyar NIPR tun lokacin da yake jami’in hulɗar jama’a na hukumar kwastam.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here