Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa Sanusi Lamido Sanusi II shi ne halastaccen sarkin Kano na gaskiya da gwamnati da al’ummar jihar ke amincewa da shi.
Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a wajen bikin yaye dalibai karo na huɗu na jami’ar Skyline Nigeria da aka gudanar a cibiyar Amani Event Centre da ke cikin birnin Kano, inda ya jaddada matsayinsa kan halaccin sarautar Kano.
A cewarsa, Sanusi Lamido Sanusi shi ne sarkin da jama’a da gwamnatin Kano suka sani, suka yarda da shi, kuma suke kallon shi a matsayin halastaccen mai sarautar gargajiya a masarautar Kano.
Rikicin masarautar ya samo asali tun shekarar 2019 lokacin da gwamnatin jihar ta wancan lokaci ta ƙirƙiri sababbin masarautu guda biyar, lamarin da ya rage wa Sanusi II iko yayin da yake kan karagar sarauta.
A shekarar 2020 ne aka tube shi daga sarauta, aka naɗa Aminu Ado Bayero a madadinsa, abin da ya ƙara tayar da kura a harkar masarautar Kano tare da raba ra’ayoyin al’umma da masu ruwa da tsaki.
Sai dai a shekarar 2023, gwamnatin NNPP ta warware waɗannan matakan, ta soke sababbin masarautun da aka ƙirƙira, tare da mayar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano kamar yadda yake a baya.
Duk da haka, batun halaccin sarautar ya ƙara rikicewa, domin ana ci gaba da kai da komo a kotuna daban-daban, ciki har da babbar kotu da kotun ɗaukaka ƙara, inda ake jiran hukuncin da zai fayyace sahihancin mallakar karagar sarautar Kano.













































