Aminu Bala Madobi
Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a zauren majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Shekarau, ya karbi katin zama dan jam’iyyar NNPP, Jamiyar dake samun hauhawa da cigaba cikin sauri.
Sanatan wanda aka zabe shi a matsayin ɗan Majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar ne biyo bayan rikicin da ya yi tsanani a cikin jam’iyyar.
Dubun dubatar magoya bayansa ne suka sheda karbar katin Sabuwar Jami’yar a gidansa da ake kira da fadar Mundubawa.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ma ya halarci gangamin taron inda ya miƙa wa Sanata Shekarau katin zama dan jam’iyyar.
Haka kuma, Dubban masu ruwa da tsaki, daruruwan magoya baya dake biyayya ga ɗariƙar Kwankwasiyya ne da shugabannin majalisar Shura na gidan Malam Shekarau da sauran masu faɗa a ji ne suka halarci taron.













































