Sallar Idi: Sarki Sanusi ya buƙaci mazauna Kano su guji tashin hankali

WhatsApp Image 2025 06 06 at 11.10.15 750x430

Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kara ba da hadin kai da goyon bayan hukumomin tsaro wajen yaki da matsalar rashin tsaro, musamman ma matsalar ‘yan daba.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya gabatar da sakon Sallah, jim kadan bayan idar da Sallar Idi a babbar filin Idi na Kano da ke kofar Mata.

Sallar ta samu halartar mataimakin gwamnan jihar Kano, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, da shugabannin gargajiya, da dubban al’ummar musulmi.

WhatsApp Image 2025 06 06 at 11.05.54 768x432

“Ina kira ga ‘yan kasa nagari da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya wajen yaki da tashe-tashen hankula, musamman yadda ayyukan ’yan daba ke karuwa a wasu sassan Kano, yana bukatar hadin kai da kuma taka tsan-tsan daga gare mu baki daya.

WhatsApp Image 2025 06 06 at 11.10.16 768x576

 

Ya kuma bukaci mazauna Kano da su kiyaye zaman lafiya, yana mai jaddada cewa Kano ta dade da sanin juna da mutunta juna a tsakanin kungiyoyi daban-daban.

WhatsApp Image 2025 06 06 at 11.04.36 1 768x576

“Bai kamata mu bar tashin hankali da rarrabuwar kawuna su lalata gadon zaman lafiya da kakanninmu suka gina ba.” a cewar Sarkin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here