Gwamnatin tarayya ta saki jerin sunayen karshe na wadanda za su amfana da afuwar shugaban ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da bayar da afuwa ta hanyar sassauta hukunci da kuma rage wasu daga cikin hukuncin da ake yi wa wasu masu laifi.
Ministan shari’a kuma babban lauya na ƙasa, Mista Lateef Fagbemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce bayan tuntubar majalisar dattawa da wasu hukumomi, shugaban ƙasa ya sake nazarin jerin sunayen da aka gabatar masa kafin amincewa da karshe.
Ya ce manufar wannan mataki ita ce tabbatar da cewa duk wanda zai ci gajiyar afuwar shugaban ƙasa ya cika dukkan ƙa’idojin doka da tsari.
A cewarsa, an cire wasu daga cikin sunayen da aka gabatar da farko saboda rashin cika sharudda, yayin da aka rage wasu hukunci domin adalci da tausayi.
Haka kuma, shugaban ƙasa ya umarci a matsar da ofishin kwamitin shawara kan afuwar shugaban ƙasa daga ma’aikatar ayyuka ta musamman zuwa ma’aikatar shari’a.
Hakan zai ba da damar fitar da sabbin ƙa’idoji don tabbatar da cewa daga yanzu ba za a sake ba da afuwa ba sai an bi tsarin doka da shawarar hukumomin gurfanarwa.
Daga cikin waɗanda aka mayar musu da hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai sun haɗa da Oroka Michael Chibueze, Adesanya Olufemi Paul, Daniel Bodunwa, Hamza Abubakar, Buhari Sani, Mohammed Musa, Muharazu Abubakar, Ibrahim Yusuf da Saad Ahmed Madaki.
Wadanda aka ba su cikakkiyar afuwa kuwa sun haɗa da Mrs Anastasia Daniel Nwaobia, Hussaini Alhaji Umar, Ayinla Saadu Alanamu, Farouk M. Lawan, Herbert Macaulay, Janar Mamman Jiya Vatsa, Ken Saro Wiwa, Saturday Dobee da Nordu Eawo, da wasu kamar Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuale, Baribor Bera, Barinem Kiobel da John Kpuine.
Sauran wadanda aka rage musu hukunci sun haɗa da Yusuf Owolabi, Ifeanyi Eze, Ibrahim Sulaiman, Patrick Mensah, Obi Edwin Chukwu, Tunde Balogun, Lima Pereira, Erick Diego, Uchegbu Emeka Michael, da wasu da dama.
NAN













































