Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar PDP, yayin da wani ɓangare ya dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa Damagum, Ologunagba da wasu

PDP PDP 750x430

Sabon rikici ya sake kunno kai a cikin jam’iyyar (PDP) a ranar Asabar, yayin da aka samu tsagewar jam’iyyar zuwa ɓangarori biyu a cikin kwamitin aiki na ƙasa (NWC) na jam’iyyar.

Wani ɓangare da ke goyon bayan ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ne ya sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, jakada Umar Damagum, tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar.

Tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda ke magana da manema labarai a madadin ɓangaren, ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda zargin rashin kwarewa, almundahana ta kuɗi, da kin bin hukuncin kotu daga Damagum.

Anyanwu ya kuma sanar da naɗin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (arewa ta tsakiya), Mohammed Abdulrahman, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa har zuwa lokacin da kwamitin ladabtarwa zai kammala bincike.

Ya ƙara da cewa an dakatar da wasu jami’an jam’iyyar da dama, ciki har da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, saboda fitar da sanarwa ba tare da izini ba, da mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu, Taofeek Arapaja.

Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: PDP ta dakatar da Anyanwu, Mashawarcinta, da wani jami’i

Haka kuma, an dakatar da ma’ajin kuɗin jam’iyyar na ƙasa, Daniel Woyenguikoro, saboda zargin almundahana ta kuɗi, da shugaban matasan jam’iyyar na ƙasa, Sulaiman Kadade, da mataimakin sakataren jam’iyyar, Setonji Koshoedo, na tsawon kwanaki 30, inda duka za a kai su gaban kwamitin ladabtarwa.

Sai dai wannan lamari ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan kwamitin aiki na ƙasa ƙarƙashin shugabancin Damagum ya sanar da dakatar da Sanata Samuel Anyanwu da mai ba da shawara na ƙasa, Kamaldeen Ajibade, da wasu biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here