Sabon ɗan majalisar wakilan Najeriya daga Taraba ya rasu

Ismaila Yushau Maihanci
Ismaila Yushau Maihanci

Wani sabon zababben dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya rasu ranar Juma’a 21 ga watan Afirilu 2023, da daddare.

Ismaila Maihanci wanda aka zaba domin wakiltar mazabar Jalingo da Yorro da Zing a majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Taraba ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Abuja.

Wani makusancin zababben dan majalisar ne ya tabbatar wa BBC rasuwar inda ya ce mutuwar ta girgiza iyalansa da kuma makusanta.

Ya kara da cewa wannan babban rashi ne ga al’ummar jihar Taraba.

Ba don rasuwarsa ba da zai kasance karon farko da marigayin, dan jam’iyyar PDP zai je majalisa bayan kayar da wanda ke kan kujerar, Kasimu Bello Maigari na jam’iyyar APC.

Ismaila wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar na majalisar tarayya a watan Fabarairu ya kasance daya daga cikin fitattun matasan ‘yan siyasa a jihar Taraba.

An sa ran yin jana’izarsa a ranar Asabar din nan 22 ga watan Afirilu, a Abuja.

An haifi marigayin mai shekara 37, a watan Oktoban shekara ta 1986.

Mamacin ya yi fice ne kasancewarsa dan kasuwa kuma matashin dan siyasa a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here