Rundunar yan sanda ta tabbatar da sake faɗuwar tankar man fetur a Jigawa

Tanker Explosion 712x430

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da sake fashewar wata tankar man fetur a wani gidan mai da ke Dutse babban birnin a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, inda ya ce ba a samu asarar rai ba.

Ya ce lamarin ya faru ne a gidan mai na Shakkato da ke kan titin Kiyawa.

“Bincike na farko ya nuna cewa gobarar ta tashi ne a lokacin da motar dakon mai ke kokarin fitar da man fetur daga cikin tankin zuwa rijiyar adana man da ke karkashin kasa.

Najeriya Tayi Asarar Dukiya Ta ₦67.1bn, da rayuka 100 a gobara a 2024 – Jaji

“Ba zato ba tsammani, gobarar ta tashi kuma ta zama tamkar wutar daji da ta fi karfin ma’aikatan gidan mai, inda suka sanar da hukumomi cikin gaggawa domin dakile lamarin”.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an kashe gobara daga filin jirgin sama na Dutse da kuma hukumar kashe gobara a garin Dutse suma suna wurin da lamarin ya faru inda suka yi nasarar shawo kan gobarar.

Sai dai ya ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa al’amura sun koma daidai a yankin inda mutane ke gudanar da harkokinsu na yau da kullun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here