Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da ɗaga likkafar manyan jami’anta 27 zuwa mukamin Air Vice Marshal.
Ɗaga likkafar ta su na zuwa ne a wani sabon sauyi da aka amince da shi bayan amincewar babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke.
Wannan shi ne sauyin farko tun bayan hawansa kan shugabanci.
A cewar babban hafsan sojin sama, wannan mataki na da nufin daidaita tsarin mulkin rundunar da sauye-sauyen tsaro da ake aiwatarwa a ƙasar, tare da inganta tsarin aiki da horo a manyan hedikwata da cibiyoyi na rundunar.
Daraktan hulɗa da jama’a da bayanai na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa wannan sauyi na nuna jajircewar shugaban rundunar wajen ƙara hanzarta yanke shawara, inganta shirin aiki, da ƙarfafa ɗaukar alhakin jagoranci a dukkan matakan rundunar.
A sabon tsarin, AVM Abubakar Abdullahi ya zama shugaban tsare-tsare da shirin aiki a hedikwatar rundunar sojin sama, haka kuma, AVM Adeniran Ademuwagun ya zama kwamandan cibiyar fasahar rundunar sojin sama da ke Kaduna, yayin da AVM Ibitayo Ajiboye ya zama babban daraktan kamfanin zuba jari na rundunar (NAFIL).
A sashen ayyuka da leƙen asiri, AVM Precious Amadi ya zama shugaban sashen ayyuka, yayin da AVM Nnamdi Ananaba ya karɓi shugabancin sashen leƙen asiri, sai AVM Ebimobo Ebiowe ya zama shugaban binciken ƙa’ida da aiki, yayin da AVM Ahmed Dari zai jagoranci sashen horo.
Sashen sauyi da ƙirƙira yanzu yana ƙarƙashin AVM Mohammed Ibrahim, wanda ke nuna ƙoƙarin rundunar wajen amfani da sabbin fasahohi a tsaron sama, a sashen injiniya da kayan aiki, AVM Olufemi Ogunsina ya zama shugaban injiniyoyi, yayin da AVM Michael Onyebashi ya karɓi jagorancin rundunar motsa jirage.
AVM David Pwajok ya zama shugaban sadarwa da bayanai, yayin da AVM John Ukeh ya zama shugaban tsaron cikin gida. A sashen gudanarwa, AVM Simon Peter ya zama shugaban kamfanin gine-gine da gidaje na rundunar, yayin da AVM Chidiebere Obiabaka ya zama sakataren rundunar a hedikwata.
Haka kuma, AVM Anthony Martins ya zama shugaban gudanarwa, yayin da AVM Abubakar Sule ya jagoranci rundunar kayan aiki, sai AVM Abdulrasheed Kotun da ya zama shugaban kula da gonakin rundunar.
AVM Edward Gabkwet kuma ya zama shugaban hulɗar rundunar da al’umma, yayin da AVM Osichinaka Ubadike ya zama mataimakin kwamandan cibiyar fasahar rundunar da ke Kaduna.
Sauran manyan jami’ai da suka haɗa da AVM Ahmed Bakari, Albert Bot, Idi Sani, Muhammed Suleiman, Jibrin Usman, da Japheht Ekwuribe, an tura su zuwa wasu cibiyoyi na haɗin gwiwar tsaro domin ƙarfafa haɗin kai da inganta tsaron ƙasa.
Air Marshal Aneke ya bayyana wannan sauyin a matsayin dabarar jagoranci da nufin tabbatar da daidaiton shugabanci, inganta tsari a cikin rundunar, da ci gaba da tabbatar da gyare-gyare da ke gudana.
Ya ce rundunar za ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin rundunoni, ta gina tsarin tsaro mai sauƙi da ke amfani da bayanai domin fuskantar kalubalen tsaro a ƙasar.
Wannan matakin ya zo ne bayan awa 24 da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta sanar da sauya muhallin manyan jami’anta 27, ciki har da manyan janarori 25 da kuma janar janar masu mukamin birgediya biyu.













































